logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai don yakar kalaman nuna kiyayya

2022-06-21 10:53:29 CMG HAUSA

Jiya Litinin, zaunannen wakilin Sin dake MDD Zhang Jun, ya yi jawabi a wajen kwarya-kwaryar taron MDD game da ranar adawa da kalaman nuna kiyayya, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su mutunta juna tare da yin shawarwari cikin adalci don yaki da irin wadannan kalamai.

Zhang Jun ya nuna cewa, kasar Sin na goyon bayan babban taron MDD da ya kira irin wannan taro don tunawa da rana ta farko a wannan fanni. Babban taron MDD ya zartas da kuduri a watan Yuli na shekarar 2021, inda aka mai da ranar 18 ga watan Yuni na ko wace shekara a matsayin ranar yaki da kalaman nuna kiyayya, Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka gabatar da wannan kuduri.

Zhang Jun ya nuna cewa, tinkara da kuma kawar da irin kalaman na bukatar kasashe daban-daban su nace ga mutunta juna da yin shawarwari cikin zaman daidaito. Kamata ya yi wasu kasashe su yi tunani mai zurfi su dubi kansu tare da yin watsi da girman kai da nuna bambanci, da mutunta moriyar sauran kasashe. Kada a yada kalaman nuna kiyayya da ma labarai na jabu ta hanyar fakewa da kare ‘yancin fadi albarkacin baki. Kuma ya kamata a yi hakuri da juna da kara tuntubar juna da ingiza mu’ammalar al’umma da kawar da rashin fahimtar juna, matakan da za su kasance a matsayin tushen kawar da kalaman nuna kiyayya. (Amina Xu)