logo

HAUSA

Sin tana adawa da dokar hana kayayyakin da suka shafi jihar Xinjiang shiga Amurka

2022-06-21 19:57:35 CMG Hausa

Yau ne, bisa dokar dake da alaka da Xinjiang da majalisar dokokin Amurka ta gabatar, hukumar kwastam da tsaron kan iyakoki ta kasar Amurka, ta ayyana dukkan kayayyakin da ake samarwa a yankin Xinjiang na kasar Sin a matsayin wai kayayyaki na "aikin tilas", tare da hana shigo da duk wasu kayayyaki dake da nasaba da Xinjiang cikin Amurkar.

Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yi nuni da cewa, ta hanyar fakewa da sunan "yancin dan Adam", Amurka tana nuna ra'ayi na kashin kai, da ba da kariyar cinikayya da cin zarafi, da yin mummunar illa ga ka'idoji na kasuwa, da kuma keta dokokin kungiyar cinikkaya ta duniya (WTO). Kuma kasar Sin tana adawa da hakan. (Ibrahim)