logo

HAUSA

Hidimar aika sakonni na kasar Sin ya karu da kashi 3.3 a watan Mayu

2022-06-20 11:10:36 CMG HAUSA

 

Kamfanonin dake ayyukan hidimar aika sakonni na kasar Sin ya samu bunkasuwa a cikin watanni biyar na farkon wannan shekarar, kamar yadda alkaluman da hukumar kididdigar aika sakonni ta kasar suka nuna.

A cewar hukumar, daga watan Janairu zuwa Mayun bana, kamfanonin aika sakonnin sun gudanar da ayyukan hidimomin aika kayayyaki da ya kai biliyan 40.95, inda ya karu da kashi 3.3 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara.

Adadin kudaden shigar da aka samu daga hada-hadar cinikayyar, ya kai RMB yuan biliyan 400.55, kwatankwacin dala biliyan 60 a cikin wannan wa’adi, inda ya karu da kashi 2 bisa 100 bisa na shekarar bara.

Shanghai shi ne ke sahun gaba daga cikin biranen kasar Sin ta fannin samar da kudaden shiga daga bangaren hada-hadar hidimar aika sakonnin kayayyaki a cikin watanni biyar din da suka gabata, sai biranen Guangzhou, da Shenzhen, da Jinhua da Hangzhou dake bi masa baya.

Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, adadin kudaden shigar kasar Sin a fannin aika sakonni ya karu da kashi 5.9 idan an kwatanta da na makamancin lokacin bara, adadin ya kai RMB yuan biliyan 531.78 tsakanin watan Janairu zuwa Mayu. A watan Mayu kadai, fannin ya samu bunkasuwar kashi 4.4 bisa 100. (Ahmad)