logo

HAUSA

Sin: Amurka da kasashen yamma suka haddasa matsalar 'yan gudun hijira ke ci gaba da tabarbarewa

2022-06-20 19:12:23 CMG Hausa

Ranar 20 ga watan Yuni, rana ce ta 'yan gudun hijira ta duniya karo na 22. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a wannan rana cewa, wasu kasashen yammacin duniya bisa jagorancin Amurka, sun dade suna haddasa yake-yake da hargitsi, da tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe, da haifar da matsaloli na jin kai. Su ne suka fara haddasa matsalar ‘yan gudun hijira.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 17 ga wata, kasar Birtaniya ta amince da mika mutumin da ya kafa shafin kwarmata bayanai mai suna, wato WikiLeaks Assange zuwa kasar Amurka. Kan wannan batu Wang Wenbin ya ce, shari'ar Assange tamkar wani madubi ne, kuma hakan na nuni da yadda kasashen Amurka da Birtaniyya suke munafurcin da'awar tabbatar da 'yancin 'yan jarida.

Wang Wenbin ya kara da cewa, yayin da ake ci gaba da bullo da tsare-tsare masu yawa da ke daidaita tsarin rigakafin cututtuka da shawo kan annoba yadda ya kamata, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma, yadda tattalin arzikin kasar Sin ke ci gaba da gudana, ya sa kasashen duniya kara amincewa da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. (Ibrahim)