logo

HAUSA

Wasikar da Xi ya rubuta ga mahaifinsa

2022-06-19 15:21:32 CMG Hausa

Yau ranar 19 ga watan Yuni, ranar mahaifa ce ta kasa da kasa, bari mu yi muku bayani kan labarin da ya faru tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da mahaifinsa Xi Zhongxun.

Hakika Xi Zhongxun ya kawo babban tasiri ga dansa shugaba Xi a bangarorin rayuwa da aiki, ana iya gano lamarin daga wata wasikar da ya rubuta ga mahaifinsa.

Ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2001, ranar murnar cika shekaru 88 na haihuwar Xi Zhongxun, inda daukacin iyalan Xi suka taru a gidansa domin tayashi murna, amma Xi Jinping wanda ya kasance shugaban lardin Fujian a wancan lokacin, bai koma gida ba, sakamakon aiki, don haka ya rubuta wata wasika ga mahaifinsa.

A cikin wasikar da ya rubata, Xi ya bayyana cewa, ya koyi halayya na gari daga mahaifinsa, yana mai cewa, “Kai kamar bijimi mai kwazo ne, dake aiki ba dare ba rana domin bautawa al’ummar kasa, lamarin da ya kara karfafa mini gwiwa, har na kudiri aniyyar bautawa al’ummun Sinawa a duk tsawon rayuwata.” (Jamila)