logo

HAUSA

SCMP: Amurka zata iya fadawa rikici sakamakon mummunar manufarta na neman dakile cigaban Sin

2022-06-19 15:52:45 CMG Hausa

Alamu sun gwada cewa, Amurka tana kara karfafa dabaru na irin salon da ta jima tana amfani dashi na nuna adawa ga kasar Sin, sai dai manufofin nata zasu iya jefa kasar cikin wani babban rikici, kamar yadda wani sharhi da aka wallafa a mujallar South China Morning Post (SCMP) ya bayyana.

A cewar Hossain Delwar, wani mawallafi, kana mai sharhi kan al’amurran kasa da kasa dake birnin Dhaka, na kasar Bangladesh, yace, kamata yayi jami’an Washington su sauya tunani, game da manufarsu na yakin cacar baka, inda suke daukar kasar Sin a matsayin wata babbar abokiyar takara ga Amurka, kamar yadda kasar Amurkar take hasashen fuskantar barazana daga kasar Sin game da tsarinta mai cike da kura-kurai.

Sharhin yayi nuni da cewa, Amurka tayi raguwar dabara game da komawa kan manufofinta na neman dakile cigaban kasar Sin, bisa tsohon ra’ayin siyasar da take la’akari dashi na cewa, tilas ne ta dakile duk wani yunkurin neman yin tasiri ko kuma karfin fada a ji.

Sharhin ya cigaba da cewa, da irin wadannan manufofi, duk wani yunkurin neman mayar da Beijing a matsayin saniyar ware, hadarin shine, tasirin rikicin Amurka da Sin zai iya haifar da matsalolin da ba za a taba iya kawo karshensu ba, kana zai haifar da gagarumar hasarar da ba za a iya kiyasta yawanta ba ga dukkan bangarorin, sannan har ma ga duniya baki daya.(Ahmad)