logo

HAUSA

Jakadan kasar Sin ya bukaci Amurka ta biya Afghanistan diyya

2022-06-17 10:29:13 CMG Hausa

Jami’in diflomasiyyar kasar Sin ya bayyana cewa, ya kamata kasar Amurka ta dauki alhakin yanayin da kasar Afghanistan ke ciki a halin yanzu, kuma ta dauki kwararan matakan biyan diyya bisa mawuyacin halin da mutanen Afghan ke ciki.

Sojojin Amurka sun kashe da dama daga cikin fararen hular kasar Afghanistan, ko kuma sun mutu a sanadiyyar yaki, kana gwamman miliyoyin mutanen kasar Afghan sun zama ‘yan gudun hijira, a cewar wakilin kasar Sin a ofishin jakadancin kasar Sin a MDD, ya bayyana hakan ne a Geneva a jawabin da ya gabatar a taron kwamitin kare hakkin bil adama na MDD karo na 50.

Jakadan na Sin yace, kasar Amurka ta janye dakarunta daga kasar Afghanistan cikin gaggawa, inda ta bar mutanen kasar cikin matsanancin halin bukatar tallafin jin kai wanda ke cigaba da faruwa har zuwa yanzu.

Ya kara da cewa, maimakon ta dauki nauyin warware matsalolin dake faruwa, Amurka ta kwashe dukiyar al’ummar kasar Afghanistan kuma ta kara jefa al’ummar kasar Afghanistan cikin mawuyacin hali.

A cewar jakadan, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gaggauta janye takunkuman da ta azawa kasar Afghanistan bisa ra’ayin kashin kanta, kuma ta mayarwa al’ummar kasar Afghanistan dukiyar kasarsu ba tare da gindaya wasu sharruda ba, sannan ta dauki kwararan matakan biyansu diyya.(Ahmad)