logo

HAUSA

A bana ne Sin ta samu sakamako mai kyau wajen sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS

2022-06-17 19:40:58 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, shekarar bana shekara ce da Sin ta samu sakamako mai kyau wajen sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS. Bisa goyon bayan bangarori daban daban, kasar Sin ta gudanar da taruka da bukukuwa fiye da 70 cikin nasara a matsayin kasar dake shugabancin BRICS a wannan karo, matakin da ya taimaka wajen yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS a fannoni daban daban.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, an samu sakamako mai kyau a fannonin siyasa, da tattalin arziki da cinikayya, da mu’amalar al’adu, da samun bunkasuwa mai dorewa, da kiwon lafiyar al’umma da sauransu, wadanda suka ba da gudummawa ga raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS, da aza tubalin shirya taron shugabannin kasashen BRICS karo na 14. (Zainab)