logo

HAUSA

Faransa da Jamus zasu karfafa tallafin soji ga Ukraine

2022-06-17 11:09:54 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya rawaito cewa, shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz sun bayyana Kiev, babban birnin kasar Ukraine a ranar 16 ga wata cewa, kasashen biyu zasu karfafa taimako a fannin aikin soji ga kasar Ukraine. A nashi bangare, Dmitry Anatolyevich Medvedev, mataimakin shugaban majalisar tsaron kasar Rasha, ya bayyana a wannan rana cewa, ziyarar da shugabannin yammacin duniyar suka kai kasar bata da wani amfani, kuma ba zata taimakawa wajen kawo zaman lafiya ga Ukraine ba.

A cewar wasu labarai daga shafin intanet na shugaban kasar Ukraine, shugaban kasar Volodymyr Zelensky, ya gana da shugabannin kasashen Faransa, da Jamus, da Italy, da Romaniya a wannan rana, domin tattauna wasu batutuwa, ciki har da batun yadda za a kara karfafa karfin tsaron kasar Ukraine, da kara sanya takunkumai da matsin lamba kan Rasha, da kuma yadda za a kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin Ukraine da kasashen Turai.(Ahmad)