logo

HAUSA

An bude dandalin tattalin arziki na kasa da kasa na St. Petersburg karo na 25

2022-06-16 12:23:00 CMG Hausa

A ranar Laraba aka bude taron dandalin tattalin arziki na kasa da kasa na St. Petersburg karo na 25 a St. Petersburg, birni na biyu mafi girma na kasar Rasha.

Taken taron shi ne, “sabbin damammaki ga sabuwar duniya,” a wannan shekarar, taron ya samu halartar wakilan kasashen duniya sama da 90 da shiyyoyi, kamar yadda mashirya taron dandalin suka bayyana.

Mahalarta taron, za su tattauna batutuwan dake shafar tattalin arzikin duniya da na Rasha, da batun ci gaban zamani, da samar da tsaron bayanai.

Mai taimakawa fadar Kremlin, Yuri Ushakov, ya sanar a jiya Laraba cewa, a jawabin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai gabatar a wajen taron dandalin a ranar Juma’a, shugaban zai yi dubi game da yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki, tare da bayyana alkiblar ci gaban tattalin arzikin Rasha a nan gaba.

Tun a shekarar 1997, dandalin ya kasance a matsayin wani muhimmin wajen tattauna muhimman batutuwan dake shafar tattalin arzikin duniya, wanda ke shafar kasar Rasha, da sabbin kasuwanni masu tasowa, da batutuwan kasa da kasa.(Ahmad)