logo

HAUSA

Sin da Kenya sun amince su zurfafa hadin gwiwarsu

2022-06-16 14:23:18 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana sakataren harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da sakatariyar harkokin wajen kasar Kenya, Raychelle Omamo, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Wang ya ce, kasar Sin tana matukar farin ciki bisa ga kakkarfan goyon bayan da Kenya ke bayarwa game da batutuwan dake shafar muhimmiyar moriyar kasar Sin, kuma a shirye take ta yi aiki tare da kasar Kenyan, don aiwatar da sakamakon da aka samu a taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika karo na takwas.

A cewar Wang Yi, duniya tana matukar fuskantar kalubaloli, har da barazanar rarrabuwar kawuna, inda ya yi nuni da cewa, wasu daga cikin kasashen duniya suna daukar matakai na kashin kansu, da nuna mulkin danniya, da sunan huldar bangarori daban-daban da demokaradiyya, kana suna kokarin haifar da koma baya game da tsarin da duniya ke bi har ma da saba dokokin kasa da kasa.

Ya ce, Kenya, a matsayinta na kasa mai matukar tasiri a Afrika, a ko da yaushe, tana taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa.

A nata bangaren, Omamo ta bayyana cewa, kasar Sin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwar Afrika ce, ta kara da cewa, Kenya da sauran kasashen Afrika a shirye suke su yi aiki tare da kasar Sin don aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron ministocin FOCAC karo na takwas.(Ahmad)