logo

HAUSA

Kasar Sin Tana Maraba Da Saka Jarin Waje A Harkar Nazari Da Yin Kirkire-kirkire

2022-06-16 19:59:00 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Shu Jueting, ta bayyana Alhamis din nan cewa, kasar Sin tana maraba da kamfanonin kasashen waje, da su kara yawan kudaden da suke kashewa wajen gudanar da nazari da yin kirkire-kirkire da ma kafa cibiyoyin nazari a kasar.

Shu ta bayyana haka ne, yayin da take karin haske, kan wani bincike na baya-bayan nan dake nuna cewa, yawancin kamfanoni daga kungiyar Tarayyar Turai, na ci gaba nuna imani kan aikin bincke da yin kirkire-kirkire na kasar Sin.

Kakakin ta ce, kirkire-kirkire wani muhimmin bangare ne na sabbin tsare-tsaren raya kasa na kasar Sin, kuma wani babban kuzari ne ga bunkasuwar tattalin arziki mai inganci.

Shu ta ce, godiya ga manufofinta na ci gaban kirkire-kirkire, kasar Sin ta kai matsayi na 12 a jerin alkaluman kirkire-kirkire na duniya na shekarar 2021, inda ta tashi daga matsayi na 34 a shekarar 2012. Tana mai jaddada cewa, kamfanonin ketare, ciki har da na Turai, sun ba da gudummawa ga ci gaban da aka samu, sun kuma amfana da manufar kasar Sin ta bude kofa da ci gaban kirkire-kirkire.(Ibrahim)