logo

HAUSA

Kasar Sin ta gina ababen more rayuwa na samar da hidimomin yanar gizo mafi girma a duniya

2022-06-16 12:49:52 CMG Hausa

A cikin shekaru 10 da suka gabata, ababen more rayuwa a fannin samar da hidimomin yanar gizo na kasar Sin sun samu ci gaba kwarai, inda aka gina tsarin yanar gizo mai matukar sauri wato fiber optic a Turance, da tsarin sadarwa na wayoyin salula mafi girma a duniya, kana tana kan gaba a duniya a fannin fasahar sadarwar 5G.

Bayanai sun nuna cewa, kasar Sin ta gina tashoshin sadarwar 5G miliyan 1.615, yayin da masu amfani da wayoyin salula masu fasahar sadarwa ta 5G ya kai miliyan 413. Karfinta a fannin fasahohin zamani na kara karuwa, kuma gibin dake tsakaninta da kasashen da ke sahun gaba wajen mallakar muhimman fasahohin zamani ya dada raguwa.

A halin yanzu, adadin kudin ciniki da ake biya ta wayar salula a ko wace shekara a kasar Sin ya kai RMB yuan triliyan 527. Kana ana kara amfani fasahar 5G da sauran wasu sabbin fasahohin sadarwa a fannoni da yawa, ciki har da masana'antu, tashar jiragen ruwa, mahakar ma'adinai, kiwon lafiya, ilmantarwa, da al’adu da kuma yawon shakatawa da dai sauransu. (Mai fassara: Bilkisu)