logo

HAUSA

Guterres ya yi Allah wadai da harin baya bayan nan a Burkina Faso

2022-06-16 10:01:10 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da kakkausar murya game da hari na baya bayan nan da aka kai a Burkina Faso, wanda ya yi sanadiyyar halaka fararen hula da dama.

A wata sanarwa, kakakin babban sakataren Stephane Dujarric, ya bayyana cewa, Guterres ya mika sakon ta’azziya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, da kuma mutanen kasar Burkina Faso.

A cewar Dujarric, mummunan harin ya faru ne a daren 11 ga watan Yuni, a garin Seytenga dake yankin Sahel na kasar Burkina Faso, wanda ya yi sanadiyyar rayukan fararen hula sama da goma, kana ya tilasta wasu da dama kauracewa gidajensu.

Jami’an tsaro a Burkina Faso sun bayyana cewa, tun bayan shekarar 2015, mutane sama da 1,000 sun rasu sakamakon hare-haren da aka kai a fadin kasar, kana sama da mutane miliyan 1.9 suka kauracewa gidajensu. (Ahmad)