logo

HAUSA

Kusan kasashe 70 sun bayyana adawa da tsoma baki cikin harkokin gidan Sin

2022-06-15 11:33:35 CMG Hausa

Kusan kasashe 70 ne suka bayyana adawa da amfani da batutuwan hakkin dan adam wajen tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin.

Kasashen sun bayyana haka ne yayin taro na 50 na majalisar kare hakkin dan adam ta MDD dake gudana a Geneva.

A madadin dukkan kasashen, kasar Cuba ta bayyanawa majalisar cewa, batutuwan HK da Xinjiang da Tibet, batutuwa ne na cikin gidan kasar Sin. Don haka, suna adawa da siyasantar da batutuwan kare hakkokin dan adam da nuna fuska biyu da katsalandan cikin harkokin kasar Sin.

A jawaban da suka gabatar ga majalisar a mabanbantan lokuta, sama da kasashe 20 sun bayyana fahimtarsu game da matsayar kasar Sin tare da goya mata baya. (Fa’iza Mustapha)