logo

HAUSA

Yunkurin wasu kasashen yammacin duniya na tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin bai yi nasara ba

2022-06-15 19:42:52 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, a gun taro na 50 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD dake gudana a Geneva, kasashe kusan dari daya sun nuna goyon bayansu ga matsayin Sin kan batun jihar Xinjiang, da yankin Hong Kong, da yankin Tibet, kuma yunkurin wasu kasashen yammacin duniya na tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin bai yi nasara ba. Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, wannan batu ya shaida cewa, wadannan kasashen yammacin duniya ne suka yi biris tare da keta hakkin dan Adam. Sun kyale matsalolinsu na keta hakkin dan Adam, amma suna zargin sauran kasashe kan batun.

Ban da wannan kuma, Wang Wenbin ya bayyana cewa, batun wai tilasta aikin kwadago a jihar Xinjiang, jita-jita ce da wasu daidaikun makiya kasar Sin suka kitsa wadda kuma ta sabawa hankali, da gaskiya da kuma ka’idoji na doka. Ba a tilasta yin kwadago a jihar Xinjiang, ma’aikatan kabilu daban-daban na jihar Xinjiang, suna zabar sana’o’insu ne bisa burinsu, da dokokin kasar Sin ciki har da dokar kula da kwadago, inda suke daddale kwangila tare da kamfanoni bisa doka da samun kudin shiga, kana suna da ‘yancin zabar wuraren da suke so su yi aiki. (Zainab)