logo

HAUSA

Ya kamata majalisar kula da hakkin dan adam ta kasance dandalin hadin gwiwa da tattaunawa

2022-06-15 10:51:54 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin a ofishin MDD dake Geneva, Chen Xu, ya ce kamata ya yi tsare tsaren kare hakkin dan adam da ya shafi kasa da kasa su kasance wani dandali na hadin gwiwa da tattaunawa, maimako na rarrabuwar kai da fito-na-fito.

Chen Xu ya shaidawa taro na 50 na majalisar kare hakkin dan adam dake gudana cewa, a shekarun baya-bayan nan, ana kara shigar da batun siyasa da fito-na-fito a majalisar, haka kuma bayanan bogi na karuwa, abubuwan da ya ce sun saba da ainihin manufarta.

Ya ce ya kamata dukkan bangarori su inganta hulda tsakaninsu a fannin kare hakkin dan adam da daukaka ka’idojin daidaito da rashin bangaranci da zabe da kaucewa siyasa da hada hannu wajen inganta manufar kare hakkokin jama’a a duniya. (Fa’iza Mustapha)