logo

HAUSA

Babban Jami'in Kasar Sin Zai Jagoranci Taron Tsaro Na BRICS

2022-06-15 20:18:56 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya sanar da cewa, za a gudanar da taron masu ba da shawara kan harkokin tsaron kasa da manyan wakilai kan harkokin tsaro na kasashen BRICS karo na 12.

Wang Wenbin ya shaidawa taron manema labaran da aka saba shiryawa Larabar nan cewa, darektan ofishin kula da harkokin kasashen waje na kwamitin tsakiya na JKS Yang Jiechi, shi ne zai jagoranci taron daga nan birnin Beijing, yayin da masu ba da shawara kan harkokin tsaron kasa da manyan wakilai kan harkokin tsaron kasa na kasashen Afirka ta Kudu, da Brazil, da Rasha da Indiya za su halarci taron.(Ibrahim)