logo

HAUSA

Sin: 'Yan Siyasar Amurka Sun Kakaba Takunkumi Marasa Ma'ana Kan Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

2022-06-14 19:44:25 CMG Hausa

A ‘yan kwanakin nan ne,‘yan majalisar dokokin kasar Amurka daga jam’iyyun siyasar kasar biyu, suka amince da shawarar da za ta bai wa gwamnatin Amurka sabbin karfi na dakile zuba jarin da darajarsu ta kai biliyoyin dalaloli da Amurka za ta yi a kasar Sin.

Kan wannan batu ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labaran da aka saba gudanarwa yau Talatar nan cewa, kasar Sin tana adawa da yadda kasar Amurka ta yiwa manufar tsaron kasa gaba daya kudin goro, tana ci gaba da karfafa bitar zuba jari da ko kadan bai dace ba, kana tana haifar da matsaloli da cikas ga harkokin tattalin arziki da cinikayya da hadin gwiwar kamfanoni daga kasashe daban daban, ciki har da kamfanonin Sin da Amurka. Hakika wannan mataki, ya kawo illa ga tsarin tattalin arziki da ciniki da ka'idojin cinikayya na kasa da kasa, kuma yana yin barazana matuka ga daidaiton tsarin masana'antu da samar da kayayyaki a duniya baki daya. 'Yan siyasar Amurka sun kakaba takunkumi kan hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci na yau da kullun tsakanin Sin da Amurka, ba tare da wasu hujjoji ba, kuma hakan ba zai iya hana ci gaban kasar Sin ba. Sai ma ya mayar da su saniyar ware da rasa damammaki na samun ci gaba. (Ibrahim)