logo

HAUSA

Kasar Sin ta dauki kaso 30 na kayayyakin da ake sarrafawa a duniya

2022-06-14 14:19:34 CMG Hausa

Alkaluman tantance ayyukan masana’antu sun nuna cewa, yayin da masana’antun sarrafa kayayyaki na kasar Sin ke kara girma da karfi, kasar ta dauki kaso 30 na jimilar kayyakin da aka sarrafa a shekarar 2021, wanda ya karu daga kaso 22.5 da ya kasance a shekarar 2012.

Mataimakin ministan ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, Xin Guobin, ya ce darajar kayayyakin da aka sarrafa ta karu daga yuan triliyan 16.98, kwatankwacin dala triliyan 2.5 a shekarar 2012, zuwa yuan triliyan 31.4 a shekarar 2021.

Ya ce duk da cewa rikice- rikicen dake gudana a yankunan duniya da sake barkewar annobar COVID-19, sun haifar da koma baya ga tattalin arzikin bangaren masana’antu, tasirinsu na wucin gadi ne.

Daga mahanga mai nisan zango, za a fahimci cewa, ginshikan cikakken tsarin sarrafa kayayyaki na kasar Sin, bai sauya ba. (Fa’iza Mustapha)