logo

HAUSA

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Kara Zurfafa Hadin Gwiwa Da Koriya ta Kudu Da Japan

2022-06-14 21:48:57 CMG Hausa

Talatar nan ce, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya aike da sakon taya murna ga taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa tsakanin kasashen Sin da Koriya ta Kudu da kuma Japan, inda ya yi kira da a kara zurfafa hadin gwiwa da kasashen 3 dake makwabtaka da juna.

Taron wanda sakatariyar hadin gwiwa tsakanin kasashen uku (TCS) ya karbi bakunci, ya kasance wani tsarin hadin gwiwa ne tsakanin kasashen Sin, da Koriya ta Kudu da kuma Japan, da fatan yayata zaman lafiya da makomar bai daya a yankin.

A cikin sakonsa, jami’in na kasar Sin ya bayyana cewa, kasashen uku suna da muradu iri daya. A cikin shekaru 20 da suka gabata, kasashen 3 sun ci gaba da yin hadin gwiwa a aikace, kuma sun kiyaye zaman lafiya da ci gaba a yankin gabashin Asiya.

A yayin da duniya ke fuskantar kalubale, Wang Yi ya bukaci kasashen uku, da su kara amincewa da juna a fannin siyasa, da fadada hadin gwiwa wajen kiyaye zaman lafiya.(Ibrahim)