logo

HAUSA

Sin na son hada kai da sauran mambobin hukumar WTO domin dakile gurbatar muhalli daga robobi

2022-06-14 11:32:55 CMG Hausa

 Zaunannen wakilin kasar Sin dake hukumar kula da cinikayya ta duniya wato WTO Li Chenggang, ya bayyana a birnin Geneva na kasar Switzerland jiya Litinin cewa, kasar Sin tana son hada kai da sauran kasashe mambobin hukumar, domin dakile matsalar gurbatar muhalli daga robobi.

Jami’in ya yi tsokacin ne yayin taron ganawa da manema labarai da aka kira bayan taron ministocin hukumar kan batun kiyaye muhalli, inda ya bayyana cewa, ya dace daukacin kasashen duniya su hada kai domin dakile kalubalen da suke fuskantar, yana mai cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan aikin dakile matsalar gurbatar muhalli daga robobi.

Ya kara da cewa, samun ci gaba mai dorewa muradin kasar Sin ne yayin da take kokarin ciyar da tattalin arzikinta gaba, kuma a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta fitar da wasu manufofi domin rage kazantar roba, kuma tana son yayata fasahohin da ta samu ga sauran kasashe mambobin hukumar WTO. (Jamila)