logo

HAUSA

Yang Jiechi ya gana da mai taimakawa shugaban Amurka kan harkokin tsaron kasa

2022-06-14 10:28:22 CMG Hausa

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin tsakiyar JKS Yang Jiechi, ya gana da mai taimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa, Jake Sullivan a Luxembourg jiya Litinin, inda suka tattauna kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da batutuwan dake jan hankulansu duka.

Yayin ganawar ta su, Yang Jiechi ya yi nuni da cewa, cikin ‘yan watannin da suka gabata, kasar Amurka ta rika danne kasar Sin a dukkan fannoni, lamarin ba zai iya warware matsalolin da Amurkar ke fuskantar ba, haka kuma zai jefa huldar dake tsakaninta da kasar Sin cikin mawuyacin yanayi. Ya ce za a iya cewa, matakin da Amurka ta dauka bai dace da moriyar sassan biyu ba, haka kuma bai dace da moriyar sauran kasashen duniya ba. Don haka, kamata ya yi Amurka ta kara fahimtar yanayin da kasar Sin ke ciki, ta yi zabin da ya dace, ta yadda za a tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma.

Kana Yang Jiechi ya jaddada cewa, kasar Sin ba za ta yarda da tsoma baki cikin harkokin gidanta ba, kuma matakan da aka dauka domin lalata dinkewar kasar Sin ba za su yi nasara ba, don haka, dole ne Amurka ta amince da ka’idar kasar Sin daya kacal a duniya, da yarjejeniyoyi uku da Sin da Amurka suka daddale. Har ila yau, dole ne Amurka ta daidaita batun dake shafar yankin Taiwan na kasar Sin ta hanyar da ta dace. Ban da haka, Yang Jiechi ya kara da bayyana matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi yankunan Xinjiang da Hong Kong da Tibet da na tekun kudancin kasar da addinai da sauransu.

Hakazalika, sassan biyu sun yi musanyar ra’ayi kan batun Ukraine da batun makaman nukiliya na kasar Koriya ta Arewa da sauransu. (Jamila)