logo

HAUSA

MDD ta yi kira da kawo karshen wariyar launin fata

2022-06-14 11:14:27 CMG Hausa

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a yi kokarin kawar da wariyar launin fata da nuna bambamci.

A sakonsa, yayin da ya rage kwanaki 100 gabanin ranar zaman lafiya ta duniya dake gudana ranar 21 ga watan Yunin kowacce shekara, Antonio Guterres, ya ce cikin kwanaki 100 masu zuwa da ma ranekun da za su biyo baya, a hada hannu wajen kare hakkin dukkan mutane da gina al’umma mai zaman lafiya da ta kunshi kowa. Ya ce idan aka hada hannu tare, za a iya cimma burin samun duniyar da babu wariyar launin fata a cikinta.

Taken ranar a bana shi ne “kawo karshen wariyar launin fata. Samar da zaman lafiya”.

Ya kara da cewa, wariyar launin fata na gurbata al’ummomi da bada dama ga nuna wariya da barkewar rikici. Don haka, dole ne a yake shi ta hanyar kawo karshen kalaman kiyayya da bada dama ga tattaunawa da shawo kan tushen matsalolin da ke haifar da rashin daidaito.

Ranar wadda ake kira da ta Zaman Lafiya ta Duniya, rana ce da MDD ta ayyana a matsayin na hutu domin tabbatar da zaman lafiyar duniya, musammam domin kawar da yaki. A kan kuma tsagaita bude wuta na wucin gadi a wuraren yaki domin bada damar kai agajin jin kai. (Fa’iza Mustapha)