logo

HAUSA

An bude taron ministocin WTO na 12 a Geneva don daidaita manyan batutuwa

2022-06-13 10:55:54 CMG Hausa

Kungiyar kasuwanci ta duniya WTO ta bude taron ministocinta karo na 12 wato (MC12) a ranar Lahadi, a helkwatar kungiyar dake birnin Geneva, na kasar Switzerland.

A lokacin taron wanda za a shafe kwanaki hudu, ana sa ran mambobin kungiyar za su tattauna muhimman batutuwa da dama, kamar batun al’amurran kasuwanci masu alaka da kare hakkokin mallakar fasahar kira wato TRIPS a takaice, da ba da izinin amfani da fasahohi don samar da riga-kafin annobar COVID-19, da batun yaki da annobar, da samar da rangwame a fannin kiwon kifi, da aikin gona, da magance matsalar abinci, da kuma yin garambawul ga ayyukan WTO da wasu muhimman ayyukan da zata bada fifiko kansu a nan gaba.

Darakta janar ta kungiyar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce a halin yanzu, duniya na fuskantar tarin matsaloli, kamar batun yaduwar annoba, da matsalar karancin abinci, da matsalolin sauyin yanayi da rikice-rikice a shiyyoyi, sannan ta yi kira ga dukkan bangarori da su yi aiki tare don kawo karshen wahalhalun da ake fuskanta.

Madam Ngozi ta ce, babu wata kasar da za ta iya magance wadannan matsaloli ita kadai, lokaci ya yi da ya kamata duniya ta dunkule don yi aiki tare. (Ahmad)