logo

HAUSA

Wasikar shugaba Xi ga jaridar HK ta nuna kulawa da burinsa kan kafafen yada labaran yankin

2022-06-13 12:17:15 CMG Hausa

An bayyana wasikar da Xi Jinping ya aikewa jaridar Ta Kung Pao ta yankin Hong Kong, a matsayin wadda ta nuna kulawarsa ga jaridar da mambobin rukunin kafafen yada labarai da jaridar ke karkashinsa. Haka kuma, ta nuna kwarin gwiwar da yake ba kafafen yada labaran HK dake kaunar kasar Sin da yankin, da kuma burin da yake da shi na ganin HK ta bude wani sabon babi.

Kakakin ofishin dake kula da yankunan HK da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin ne ya bayyana haka a jiya.

Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasa kuma shugaban rundunar sojin kasar Sin, ya aike da wasika ga jaridar Ta Kung Pao ta HK ne a jiya, domin taya ta murnar cika shekaru 120 da kafuwa. (Fa’iza Mustapha)