logo

HAUSA

Masu bada taimako na kasar Sin sun bayar da kwarin gwiwa ga dalibai matasa na makarantun Kenya

2022-06-13 10:23:19 CMG Hausa

Masu bayar da taimako na kasar Sin suna bayar da kwarin gwiwa ga matasan dake karatu a makarantar Mcedo Beijing dake yankin Mathare a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Yaran wadanda marasa galihu ne, sun samu damar shiga makarantar wacce ke yankin gabashin birnin Nairobi, sun yabawa taimakon da suka samu daga masu bada taimako na kasar Sin, inda aka kashe musu kishirwar da suka shafe shekaru da dama tana damunsu na burin samun ingantaccen ilmi.

Naftali Kizito, wani dalibin aji na 8 na makarantar Mcedo Beijing, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a lokacin tattaunawar da aka yi da shi a baya bayan nan cewa, taimakon da kasar Sin ta bayar ya sauya yanayin makarantarsu, inda ta koma wata cibiyar koyarwa irin ta zamani.

Kizito ya ce, gabanin bayar da gudunmawar, dakunan karatun da suke amfani da su na wucin gadi ne. A yanzu an yi musu gine-gine wadanda suke jin dadin koyon karatu a cikinsu.

A shekarar 2007, ofishin jakadancin kasar Sin a Kenya ya samar da kudaden gudanar da aikin gina makarantu na zamani a makarantar Mcedo Beijing.

Daga bisani a shekarar 2012, sakamakon shirin da ofishin jakadancin Sin ya bullo da shi a Kenya, kungiyar hadin gwiwar bunkasa tattalin arziki da kasuwanci ta Sin da Kenya wato (KCETA), ta tsara wasu kamfanonin kasar Sin ta dama, kana ta samar da kudaden tallafawa aikin fadada makarantar. (Ahmad)