logo

HAUSA

Kimiyya da fasaha na bunkasa bangaren sufurin kasar Sin

2022-06-13 11:43:06 CMG Hausa

Kasar Sin na samun muhimman nasarori a fannin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a bangaren sufuri, wadanda bangarorin sufurin jiragen kasa masu sauri da jiragen ruwa da na sama, har ma da tsarin jigilar kai sakonni suka shaida.

A bangaren sufurin jiragen kasa, mizanin fasaha da kwarewar Sin ya shiga muhimmin matsayi a duniya. Misali, jirgin kasa mai matukar sauri dake zirga-zirga tsakanin biranen Beijing da Zhangjiakou na jigilar fasinjoji kai tsaye ba tare da matuki ba, inda yake tafiyar kilomita 350 a kowacce sa’a. A bangaren sufurin jiragen sama kuwa, filayen jiragen sama 234 na kasar na hidimtawa fasinjoji ta hanyoyin na’urorin zamani, wato fasinjoji ba sa bukatar takardu kamar tikiti, lamarin da ya kara ingancin tsaron matafiya da kaso 30. A fannin jigilar kayayyaki kuwa, an hada tsarin kai sakonni da cinikayya ta intanet, lamarin dake taimakawa wajen sayar da kayayyakin sama da CNY triliyan 10 a shekara. Wannan tsari ya zama mai gaggauta rarraba kayayyaki tare da zama babbar hanyar hidimtawa masu sayayya ta intanet.

Hakika, kasar Sin na samun ci gaban fasahohohin zamani da ingancin tsarin sufuri cikin sauri, wanda ke karfafa ginin ababen more rayuwa masu dacewa da kyautata muhalli da inganta hade tsarin raya ababen sufuri da bayanai da makamashi da tsimin ruwa da sauransu. (Fa’iza Mustapha)