logo

HAUSA

Sin ta gudanar da ayyukan nazarin kayan tarihi fiye da 8800 a cikin shekaru 10 da suka gabata

2022-06-12 17:06:02 CMG Hausa

Ranar Asabar ta biyu ta watan Yuni na kowace shekara, rana ce ta kayayyakin al’adu da halittu da aka gada daga kaka da kakanni ta kasar Sin. A jiya ne, aka bude bikin ranar kayayyakin al’adu da halittu da aka gada daga kaka da kakanni ta kasar Sin ta shekarar 2022 a lardin Gansu, a yayin bikin budewar, hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin ta bayyana cewa, Sin ta gudanar da ayyukan nazarin kayan tarihi fiye da 8800 a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Taken ranar ta wannan shekara, shi ne tabbatar da tsaron kayan tarihi don more al’adu da ilmi tare da jama’a a zamanin yanzu. Shugaban hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin Li Qun ya bayyana a jawabin da ya gabatar cewa, kayan tarihi albarkatun al’adu ne na kasar Sin da ba za a iya sabunta su ko maye gurbinsu a nan gaba ba, kana su ne farkon wayewar kan kasar Sin na samun wadata da farfadowar al’ummar kasar. Don haka, ya kamata a ci gaba da gudanar da ayyukan neman kayan tarihi da ilmin al’adun kasar Sin, da tabbatar da tsaronsu, da shaidawa duniya kimar kasar Sin na yin imani, da nuna kauna da kuma girmama ta. (Zainab)