logo

HAUSA

Xi Ya Taya Ta Kung Pao Murnar Cika Shekaru 120 Da Kafuwa

2022-06-12 19:50:57 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga Ta Kung Pao, daya daga cikin tsoffin jaridun Sinanci dake zaune a Hong Kong, murnar cika shekaru 120 da kafuwa.

A cikin wasikar tasa, shugaba Xi ya bukaci jaridar da ta ci gaba da gudanar da al'adunta na kishin kasa, da neman ci gaban kirkire-kirkire, da kuma rubuta manyan babuka masu ban sha'awa na ci gaba da aiwatar da manufar nan ta “kasa daya, amma tsarin mulki biyu” yadda ya kamata.(Ibrahim)