logo

HAUSA

Yawan fasinjojin da aka yi jigilar su ta jiragen sama a kasar Sin ya kai 33.1% bisa adadin dukkan sufuri a kasar

2022-06-12 16:56:00 CMG Hausa

A cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu bunkasuwar sha’anin sufurin jiragen sama na kasar Sin sosai, yawan fasinjojin da aka yi jigilar su ta jiragen sama ya kai kashi 33.1 cikin dari bisa adadin dukkan sufurin kasar. Sin ta daddale yarjejeniyoyin jigilar jiragen sama tare da kasashe da yankuna 128, da bude hanyoyin jiragen sama 895 a tsakaninta da kasashen waje.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, an gina sabbin filayen jiragen sama ko canja wurin filayen jiragen sama 82 a kasar Sin, a halin yanzu yawan filayen saman kasar Sin ya kai 250, yawan mutanen da ake jigilar su ta jiragen sama ya zarce biliyan 1 da miliyan 400. An bude sabbin hanyoyin jiragen sama fiye da 3000, yawansu a kasar Sin ya zuwa yanzu ya kai 5581. Kana ana iya zuwa kaso 92 cikin 100 na sassan kasar Sin ta jiragen sama, kana kashi 88 cikin dari na Sinawa na iya tafiya ta jiragen sama. An kuma gina sabbin filayen jiragen sama a yankuna masu fama da talauci 47, an kuma samar da hidimar sufurin jiragen sama ga mutanen da yawansu ya kai kashi 83.6 cikin 100 a wadannan yankuna. (Zainab)