logo

HAUSA

An gudanar da zanga-zangar nuna adawa da harbe-harben bindiga a Washington da wasu sassan Amurka

2022-06-12 16:33:46 CMG Hausa

 

Daruruwan masu zanga-zangar ne, suka shirya zanga-zanga a birnin Washington, D.C. da ma fadin kasar Amurka a jiya Asabar, inda suke kira ga ‘yan majalisar dokokin kasar, da su amince da dokar da za ta kawo karshen tashe-tashen hankula masu nasaba da harbe-harben bindiga, biyo bayan wasu dalibai da aka kashe a watan jiya a wata makarantar firamare dake jihar Texas.

Tattakin mai taken “March for Our Lives (MFOL)”, kungiyar masu yaki a harbin bindiga wadda daliban da suka tsira daga kisan kiyashin shekarar 2018 a wata makarantar sakandare ta Parkland a jihar Florida, suka kafa ta ce ta shirya gangami sama da 450 a ranar Asabar, ciki har da New York, da Los Angeles da kuma Chicago.

A birnin Washington, daruruwan mutane ne, suka taru a babban fili na kasa da ke kusa da dandalin tunawa da Washington cikin yayyafi na ruwan sama.

Tattakin da kungiyar ta shirya a shekarar 2018 a Washington, makonni bayan kashe mutane 17 a makarantar sakandare ta Marjory Stoneman Douglas da ke Parkland, ya hallara dubban daruruwan mutane zuwa babban birnin kasar, don matsawa majalisa lamba, kan ta dauki matakin doka, ko da yake 'yan Republican dake adawa, sun hana duk wata sabuwar doka dake iyakance shekarun mallakar bindiga da dai sauransu daga samun amincewa a majalisar dattawa.

Ganganim na bana da aka shirya a Washington, ya aike da sako mai sauki ga shugabannin siyasar kasar, a cewar masu shirya shi: Rashin daukar mataki a bangarenku, yana kashe Amurkawa.(Ibrahim)