logo

HAUSA

Ghana zata shuka bishiyoyi miliyan 20 don farfado da gandun daji

2022-06-11 18:37:47 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Ghana ta sanar a ranar Juma’a cewa, ta kudiri aniyar shuka bishiyoyi kimanin miliyan 20 a wannan shekarar domin farfado da dukkan gandun dajin dake fadin kasar.

Shugaban kasar, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bayyana hakan a wajen kaddamar da shirin dashen itatuwa a babban birnin kasar, domin tunawa da ranar samar da muhallin launin kore ta kasar Ghana karo na biyu.

Akufo-Addo, wanda ya dasa bishiyar madaci ta Afrika, ya bukaci dukkan mutanen kasar Ghana, da su shuka a kalla bishiya daya zuwa uku a wannan shekarar, domin taimakawa kasar wajen cimma nasarar ajandar samar da koren mahalli don farfado da dazukan da suka durkushe a kasar.

Akufo-Addo yace, "Ghana ta daura damarar yin galaba a shirin yaki da sauyin yanayi, da kuma samar da wadatar abinci a kasar, inda ya bayyana bishiyoyi da dazuka a matsayin albarkatun da suka zama tilas ga rayuwar dan adam a duniya, da kuma samar da ingantacciyar lafiyar yanayin muhallin halittu.(Ahmad)