logo

HAUSA

Sin: Tilas Ne Amurka Da Birtaniya Da Australiya Su Amsa Tambayar Duniya Dangane Da Hadin Gwiwarsu Kan Jirgin Ruwa Karkashin Ruwa Mai Aiki Da Makamashin Nukiliya

2022-06-10 11:59:33 CMG HAUSA

Jiya Alhamis kwamitin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA ya duba illolin da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Amurka, Birtaniya da Australiya dangane da jirgin ruwan karkashin ruwa mai aiki da makamashin nukiliya a fannonin musayar abubuwan nukiliya da ba da tabbaci da kuma sa ido a kai, ta yi kan “yarjejeniyar dakile yaduwar makaman nukiliya wato NPT”.

A yayin taron, Wang Qun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD da sauran hukumomin kasa da kasa a birnin Geneva ya yi nuni da cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 3 dangane da jirgin ruwan karkashin ruwa mai aiki da makamashin nukiliya, ya saba wa yarjejeniyoyi da takardu masu ruwa da tsaki. Kasashen duniya sun rika nuna damuwa kan lamarin, don haka wajibi ne kasashen 3 su amsa tambayar kasa da kasa.

Wang Qun ya ci gaba da cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 3 dangane da jirgin ruwa karkashin ruwa mai aiki da makamashin nukiliya, ta saba wa yarjejeniyar NPT, da “yarjejeniyar IAEA ta ba da tabbaci da sa ido daga dukkan fannoni” da “karin yarjejeniyar da IAEA da Australiya suka daddale”. Kome hujjar da kasashen 3 suka yi amfani da ita wajen yin hadin gwiwa kan jirgin ruwa karkashin ruwa mai aiki da makamashin nukiliya, kome matakan da za su dauka wajen daidaita abubuwa masu nasaba da makaman nukiliya, lallai wadannan kasashe 3 sun yi musayar abubuwa masu nasaba da makaman nukiliya ba bisa doka ba.

Wang Qun ya ci gaba da cewa, Amurka da Birtaniya sun nuna fuska biyu kan dakile yaduwar sinadarin nukiliya. A wani bangare, sun sanya takunkumi na kashin kai kan wasu kasashen da ba su da makaman nukiliya, wadanda suka kirkiro da kuma samun abubuwan nukiliya ba domin aikin soja ba, amma a wani bangare na daban kuma, sun kau da ido daga Australiya, sun bai wa Australiya abubuwa masu nasaba da makaman nukiliya kai tsaye a fili. Abun da suka yi zai yi mummunar illa kan tsarin kasa da kasa na dakile yaduwar makaman nukiliya da kuma yadda ake daidaita batutuwan nukiliya na Iran da Koriya ta Arewa. (Tasallah Yuan)