logo

HAUSA

Yan bindiga sun kai hari wasu kauyuka a arewacin Najeriya sun kashe mutane 32

2022-06-10 10:01:28 CMG Hausa

A kalla mutane 32 aka kashe a farkon wannan mako a wasu hare-haren da ’yan bindiga suka kaddamar kan kauyuka uku a jahar Kaduna dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, babban jami’in jahar ya sanar da hakan.

A sanarwar da aka fitar ranar Alhamis, gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce, rahotannin da hukumomin tsaro suka bayar ya nuna cewa, maharan masu yawan gaske sun kaddamar da harin ne kan kauyukan Dogon Noma, Unguwan Sarki, da kuma kauyen Unguwan Maikori, dake karamar hukumar Kajuru a jahar a ranar Lahadi, inda suka kashe mazauna kauyuka.

Ya ce bayan faruwar harin na ranar Lahadi, hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya dake yankunan sun dinga sanar da gwamnati bayanai game da halin da ake ciki a yankunan.

A cewar gwamna El-Rufai, ’yan fashin sun kaddamar da harin farko kan kauyuka biyu, inda suka kashe mutane 31. Daga bisani suka sake kutsawa zuwa kauyen Unguwan Maikori, inda suka sake kashe mutum guda, kana sun kone gidaje da dama. (Ahmad)