logo

HAUSA

Sin:Ya kamata Amurka da NATO su yi bayani da kuma biyan diyya ga wadanda harin bama-bamai na Depleted Uranium suka shafa

2022-06-10 21:02:42 CMG Hausa

Da yake karin haske game da tuhumar da ake yiwa kungiyar tsaro ta NATO, kan wadanda harin bama-bamai na Depleted Uranium da ta kai Yugoslavia ya rutsa da su. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a taron manema labarai na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, ya kamata Amurka da kungiyar tsaro ta NATO, su yi tunani sosai kan laifuffukan yakin da suka aikata, kuma su biya diyya ga wadanda harin bam na Depleted Uranium din suka shafa ba tare da bata lokaci ba

Yau ake bikin cika shekaru 23 da kawo karshen harin bama-baman da kungiyar tsaro ta NATO ta kai tarayyar Yugoslavia. Dangane da munanan illolin da harin bama-bamai na Depleted Uranium  da suka kai nauyin tan 15 da NATO ta jefa a waccan shekarar, mutane 3,000 da harin ya shafa, sun baiwa wata tawagar lauyoyin kasa da kasa iznin shigar da kungiyar NATO kara. Sai dai kuma kungiyar NATO ta yi ikirarin cewa, tana da rigar kariya.(Ibrahim Yaya)