logo

HAUSA

Wasu shugabannin kasashen nahiyoyin Amurka sun ki halartar taron koli na nahiyar

2022-06-10 12:01:59 CMG Hausa

 

An kaddamar da taron koli karo na tara na nahiyoyin Amurka a birnin Los Angeles na kasar Amurka, a ranar 8 ga wata. Amma sakamakon rashin amincewa da manufofin harkokin waje na kasar Amurka, wasu shugabannin kasashen nahiyoyin sun ki halartar taron, wanda za a shafe kwanaki uku ana gudanarwa.

Kafin wannan, majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta ki gayyatar shugabannin kasashen Cuba, da Nicaragua, da Venezuela don halartar taron, bisa hujjar wai batun demokuradiyya. Lamarin da ya samu kin yarda daga wasu kasashen Latin Amurka, inda shugaban kasar Mexico Andrés Manuel López Obrador ya sanar da kin halartar taron, yayin da kasashen Guatemala, Honduras and El Salvador suka sanar da tura tawagoginsu masu karamin matsayi.(Kande Gao)