logo

HAUSA

Shugaban Ukraine ya amince da sanya takunkumi kan shugaban Rasha da wasu jami’an gwamnati

2022-06-10 11:54:38 CMG Hausa

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, a ranar Alhamis ya sanya hannu kan wasu dokokin biyu dake shafar sanya takunkumai kan shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, da wasu jami’an gwamnatin Rasha sama da 200, ofishin yada labaran fadar shugaban kasar ne ya sanar da daukar matakin.

Takunkuman sun shafi haramtawa shugaba Putin gudanar da dukkan harkokin cinikayya, kamar abin da ya shafi shigi da fici, da ratsawa ta  yankunan dake karkashin ikon Ukraine, da kuma shiga duk wani al’amari dake shafar cefanar da kaddarori mallakin kasar Ukraine.

Takunkuman sun kuma kunshi rike dukiyoyin Rasha, da haramta amfani da tashoshin radiyo mallakin kasar Ukraine a Rasha.

Bugu da kari, takunkuman za su yi aiki kan wasu kusoshin gwamnatin Rasha 34, ciki har da firaministan Rasha Mikhail Mishustin da kakakin gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov.

Sannan, an kuma sanya takunkuman kan wasu manyan makarantun ilimi 263.

Daga cikin matakan da aka dauka, an haramtawa makarantun ilmin kasar Rasha shirya dukkan wasu huldar raya al’adu, da kimiyya da wasanni tsakaninsu da takwarorinsu na kasar Ukraine. (Ahmad)