logo

HAUSA

Xi Jinping ya rubuta wasika ga mahalarta taron karawa juna sani na jam’iyyu shida dake kudancin Afirka da suka kafa makarantar Julius Nyerere

2022-06-09 20:53:17 CMG Hausa

Jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya rubuta sako ga dukkan mahalarta taron sanin makamar aiki na jami’ai matasa na jam’iyyu shida dake kudancin nahiyar Afirka, wadanda suka kafa makarantar koyar da harkokin shugabanci ta Julius Nyerere.

Xi ya ce, neman cimma muradun ci gaba, da farfado da al’umma da samar da alfanu ga jama’a, na bukatar jajircewar zuriyoyin al’umma. Kara gina duniya mai kyakkyawar makoma, na bukatar mu’amalar kasa da kasa.

Xi ya jaddada fatansa cewa, ya dace wadannan jami’an su dauki nauyin dake wuyansu, da nuna kwazo wajen raya sha’anin karfafa zumunta tsakanin Sin da Afirka, a kokarin bayar da gudummawarsu wajen gina al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya.

Kwanan baya, aka gudanar da taron sanin makamar aiki tsakanin jami’ai matasa na jam’iyyu shida dake kudancin nahiyar Afirka, wadanda suka kafa makarantar koyar da shugabanci ta Julius Nyerere tare a kasar Tanzaniya. Taron, mai aken “Sabon ci gaba a sabon zamani: Mu’amala da hadin-gwiwa tsakanin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da jam’iyyu shida dake kudancin nahiyar Afirka”, ya samu halartar wasu jami’ai matasa 120, wadanda suka gabatar da wasika ga shugaba Xi a karshen taron, don bayyana aniyarsu ta ci gaba da yaukaka zumunta da zurfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka. (Murtala Zhang)