logo

HAUSA

Xi yana rangadin aiki a lardin Sichuan

2022-06-09 15:37:44 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya je birnin Meishan na lardin Sichuan dake kudu maso yammancin kasar domin rangadin aiki.

Da farko, Xi wanda ya fara rangadin da safiyar jiya Laraba, ya je kauyen Yongfeng na garin Taihe na birnin, wanda ya mallaki gonaki kadada 431 da iyalai manoma 2133, domin binciken yadda kauyen yake ingiza gina gonaki masu inganci domin samun karin hatsi.

Wani jami’in kauyen ya gaya wa shugaba Xi cewa, matsakaicin kudin shigar kowanne manomin kauyen ya kai kudin Sin yuan dubu 28 a shekarar 2021, adadin da ya kai matsayi na hudu a fadin lardin Sichuan.

Hakika yayin taruka biyu na bana, shugaba Xi ya taba bayyana cewa, samar da isasshen abinci ga al’ummun kasa, shi ne aiki mafi muhimmanci ga gwamnatin kasar Sin, don haka ya bukaci a gina gonaki masu inganci kadada miliyan 66.7 a fadin kasar ta Sin. (Jamila)