logo

HAUSA

Kasar Sin za ta iya samar da kaimin farfado da tattalin arzikin duniya

2022-06-09 19:55:15 CMG Hausa

A yayin da yake karin haske kan sabon rahoton tattalin arzikin kasar Sin da babban bankin duniya ya fitar, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana Alhamis din nan cewa, yayin da ake fuskantar kalubale daban-daban a cikin gida da kuma waje, tattalin arzikin kasar Sin zai iya tabbatar da daidaito da samun ci gaba na dogon lokaci da ma ba da kwarin gwiwar daidaitawa da farfado da tattalin arzikin duniya, tare da kara samar da karfin kasar Sin.

A jiya ne dai, sabon rahoton tattalin arzikin Sin din da babban bankin duniya ya fitar ya nuna cewa, a cikin rubu'in farko na wannan shekara, tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasa sosai. Biyo bayan wasu tsare-tsare da matakai na daidaita tattalin arziki, ana sa ran saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya sake dawowa a cikin rabi na biyu na wannan shekara.