logo

HAUSA

Jam’iyyar APC ta tsayar da Tinubu a matsayin dan takararta na shugaban kasa

2022-06-09 10:09:47 CMG Hausa

Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagos dake kudu maso yammacin Nijeriya, ya lashe zaben fidda dan takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Tinubu wanda kuma jagoran jam’iyyar ne, ya yi nasara kan ’yan takara 13, ciki har da mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan, yayin babban taron jam’iyyar na kwanaki 3 da ya samu halartar shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Da yake jawabi a dandalin Eagle dake Abuja, babban birnin kasar, wato inda taron ya gudana, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ce, muhimmin aikin dake gaban jam’iyyar a yanzu shi ne, ci gaba da tabbatar da hadin kan mambobin jam’iyyar tare da cimma yarjejeniyar da ake bukata.

A nasa jawabin, Bola Ahmed Tinubu ya ce kasar mafi yawan al’umma a Afrika tana fama da tarin kalubale. Sai dai, ya lashi takobin farfado da tattalin arziki da sake gina kasar idan aka ba shi damar samun nasara a zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a watan Fabrerun 2023. (Fa’iza Mustapha)