logo

HAUSA

Firaministan Sin ya jaddada aniyar inganta harkokin sufuri da jigilar kayayyaki don daidaita yanayin tattalin arziki

2022-06-08 11:50:19 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada aniyar kara kyautata yanayin sufuri da jigilar kayayyaki domin tabbatar da gudanarwar harkokin kasuwanci da daidaita yanayin tattalin arziki.

Li ya yi wannan tsokaci ne a yayin da ya kai ziyara ma’aikatar sufuri ta kasar a ranar Litinin, inda ya bukaci a kara himma wajen daidaita yanayin yaki da annobar COVID-19, da tattalin arziki da ci gaban zaman rayuwar al’umma.

Yayin da yake duba yanayin sashen rarraba kayayyakin da ake jigilarsu ta manyan hanyoyin mota, da ta ruwa, da kuma ta sama ta kafar bidiyo, Li ya jaddada bukatar a dauki matakai don magance cinkoson kwatainoni da ake samu a tashoshin ruwa ba tare da bata lokaci ba, a yayin da ake kokarin yaki da annobar COVID-19.

Li ya ce, tattalin arzikin kasar Sin ya haifar da gagarumin tasiri kan tattalin arzikin duniya, inda ya kara jaddada aniyar daukar matakai wajen tafiyar da ayyukan hidimomin sufurin kayayyaki, da kuma kara inganta ayyukan tantance kayayyaki na hukumomin kwastom, domin kyautata ayyukan shigi da ficin kayayyaki, don daidaita ci gaban masan’antu da tsarin samar da kayayyaki.

Firaministan na Sin ya kuma bukaci gwamnatocin kananan hukumomi, da su kara karfafa tsarin ayyukansu wajen tabbatar da gudanarwar sufurin kayayyaki a manyan masana’antu, da shiyyoyi da kamfanoni, kana su taimaka don cimma nasarar bunkasar wannan fannin ba tare da bata lokaci ba, domin kafa wani muhimmin tushe na bunkasar tattalin arziki a rubu’i na biyu, da kuma dorewar ci gaban bunkasar tattalin arziki na dogon lokaci. (Ahmad)