logo

HAUSA

Xi ya kai ziyara birnin Meishan dake kudu maso yammacin kasar Sin

2022-06-08 22:12:29 CMG Hausa

Larabar nan ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Meishan na lardin Sichuan dake yankin kudu maso yammacin kasar.

Da safiyar ta yau, Xi ya ziyarci kauyen Yongfeng da San Su Ci, wurin tunawa kuma tsohon mazaunin Su Xun da 'ya'yansa maza guda biyu Su Shi da Su Zhe, mashahuran mutane uku wajen adabi na zamanin daular Song ta Arewa (960-1127).

Xi ya kuma fahimci kokarin da ake yi wajen bunkasa manyan filayen noma, da bunkasa noman hatsi, da inganta farfado da yankunan karkara, da kiyaye muhimman matakan kandagarki da dakile yaduwar COVID-19, da kiyaye kayayyakin tarihi da na al'adu.