logo

HAUSA

ECOWAS ta yi Allah wadai da harin cocin Catholic a Najeriya

2022-06-08 11:02:39 CMG Hausa

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), ta yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan cocin Catholic a Najeriya, a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar gomman rayukan masu bauta.

A sanarwar da ta fitar ranar Talata, ECOWAS ta yi Allah wadai da babbar murya game da abin da ta kira mummunan abin takaici, wanda ya haifar da sakamako mummuna daga dukkan fannoni, sannan kungiyar ta jajantawa gwamnati, da al’ummar Najeriya da iyalan mutanen da harin ta’addancin ya shafa.

Sanarwar ta bayyana cikakken goyon bayan kungiyar shiyyar ga Najeriya, ta kuma yi alkawarin ci gaba da yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki, domin kawar da ayyukan ta’addanci daga shiyyar.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, wasu gungun ’yan bindiga dauke da makamai suka kaddamar da hari kan wata coci dake garin Owo, a jahar Ondo dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, inda suka kashe a kalla masu bauta 22 tare da jikkata wasu mutanen 50. (Ahmad)