logo

HAUSA

Kasashen BRICS sun yi alkawarin zurfafa hadin gwiwarsu a fannin bayanan sirri na aikin kwastom

2022-06-08 11:49:37 CMG Hausa

Hukumomin kwastom na kasashe mambobin BRICS sun sha alwashin zurfafa hadin gwiwarsu a fannin samar da bayanan sirri kan aikin kwastom. Sun bayyana hakan ne a wani taro ta kafar bidiyo a ranar Talata.

Sun Yuning, mataimakin shugaban babbar hukumar kwastom ta kasa Sin ya ce, hadin gwiwa a fannin aikin kwastom tsakanin kasashen BRICS ya samu kyawawan sakamako tun bayan kafa tsarin hadin gwiwar a shekarar 2013, yayin da huldar kasuwanci dake tsakaninsu take ci gaba da bunkasuwa.

Alkaluman da hukumomi suka fidda ya nuna cewa, huldar cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen BRICS ta kai jimillar dala biliyan 490.42 a shekarar 2021, inda ta karu da kashi 39.2 a bisa na makamancin lokacin shekarar bara, adadin da ya zarta na dukkan huldar kasuwancin da kasar Sin ta yi da kasashen ketare a makamancin lokacin.

Domin tinkarar barazana da kuma kalubalolin da ake fuskanta a halin yanzu, mahalarta taron sun yi alkawarin tabbatar da ganin hukumomin kwastom na kasashen BRICS sun cigaba da yin aiki tare, domin kiyaye tsarin samar da kayayyaki da jigilarsu a kasa da kasa, da kuma tabbatar da saurin bunkasar tattalin arziki da farfadowar cinikayya a tsakanin kasashen BRICS. (Ahmad)