logo

HAUSA

Sin: Ba Za A Iya Kare Mata Da Yara Ba, Illa A Tsagaita Bude Wuta Da Kuma Wanzar Da Zaman Lafiya

2022-06-07 11:26:22 CMG HAUSA

Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya ce ba za a iya kare mata da kananan yara daga illolin rikicin kasar Ukraine ba, illa a tsagaita buta wuta da kuma maido da zaman lafiya. Yana mai cewa, bayar da tallafin makamai da sanya takunkumi, ba za su haifar da komai ba, sai tsawaita lokacin rikicin da kuma fadada rikicin zuwa wasu wurare.

Dai Bing ya bayyana haka ne jiya Litinin, yayin da kwamitin sulhu na MDD yake nazari kan batun cin zarafi ta hanyar lalata da kuma fataucin mutane da rikicin kasar Ukraine ya haifar.   

Dai Bing ya kara da cewa, rikicin Ukraine ya haifar da dimbin asara ga fararen hula, musamman ma mata da kananan yara, inda suke fuskantar babbar barazanar tsaron lafiyarsu, wanda ke jawo damuwa matuka. A cewarsa, kamata ya yi bangrorin da rikicin ya shafa su mutunta dokokin kasa da kasa, su dauki matakan kare fararen hula daga kowane irin nuna karfin tuwo, ciki hadda cin zarafin mata da kananan yara mata ta hanyar lalata da kuma fataucinsu.

Tun bayan barkewar rikicin, al’ummar Ukraine kimanin miliyan 6 da dubu 800, yawancinsu mata da kananan yara, sun ketare iyakokin kasar, inda suka shiga kasashe makwabta don samun mafaka.

Dai Bing ya ci gaba da cewa, kawar da cin zarafi ta hanyar lalata da kuma fataucin mutane sakamakon barkewar rikici ba za su isa ba. Ya ce ba za a iya kare mata da kanana yara daga illolin rikici ba, sai an tsagaita bude wuta da maido da zaman lafiya. Ya ce kamata ya yi kasashen duniya su hada hannu wajen kara azama kan ci gaba da yin shawarwarin zaman lafiya a tsakanin kasashen Rasha da Ukraine. Ya ce ana fatan za a warware batun abinci na Ukraine da kuma taimakawa bangarori masu ruwa da tsaki kara amincewa da juna a yayin taron da kasashen Rasha, Ukraine, MDD, da kasar Türkiye za su gudanar nan gaba ba da dadewa ba. (Tasallah Yuan)