logo

HAUSA

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mayar da martani kan korar jirgin sojan Australiya

2022-06-07 21:16:03 CMG Hausa

Game da korar jirgin sojan kasar Australiya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Talata cewa, kasar Sin tana yin kira ga Australia da ta gaggauta dakatar da irin wadannan ayyuka masu tada fitina da kuma hadari, in ba haka ba, za ta dauki dukkan munanan sakamakon da ta tayar saboda hakan.

Zhao ya bayyana cewa, “A ranar 26 ga watan Mayun da ya gabata ne wani jirgin yaki samfurin P8A na kasar Australiya, ya shiga sararin samaniyar yankin tsibiran Xisha na kasar Sin, domin yin bincike, kuma ya ci gaba da nufa sararin samaniyar Xisha na kasar Sin duk da gargadin da bangaren Sin ya yi masa. Rundunar sojan ‘yantar da jama’ar kasar Sin da aka girke a kudancin yankin ta shirya sojojin ruwa da na sama, don ganowa da kuma tantance asalin jirgin saman sojan Australiya, tare da ba da gargadin korarsa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)