logo

HAUSA

Sin: An Kaddamar Da Jarrabawar Shiga Jami’a

2022-06-07 13:42:58 CMG HAUSA

Yau Talata ne aka fara gudanar da jarrabawar shiga jami’a a sassa daban daban na kasar Sin.

Alkaluman ma’aikatar ilmi ta kasar Sin sun nuna cewa, yawan wadanda suka yi rajistar rubuta jarrabawar a bana ya kafa tarihi, inda ya kai miliyan 11.93 baki daya, wanda ya karu da miliyan 1 da dubu 150 bisa na shekarar 2021. Akwai wuraren gudanar da jarrabawar guda dubu 330 a duk fadin kasar Sin, tare da masu sa ido kimanin miliyan 1 da dubu 20. (Tasallah Yuan)