logo

HAUSA

Isra’ila ta harba makamai masu linzami kan wasu sansanonin soji a Syria

2022-06-07 10:36:17 CMG Hausa

 

Rundunar sojin Syria ta ce, dakarun Isra’ila sun harba makamai masu linzami daga yankin tsaunikan Golan da Isra’ilar ta mamaye, zuwa wasu sansanonin soji dake gabashin birnin Damascus, a daren ranar Litinin.

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta kara da cewa, an yi nasarar kakkabo makaman, kuma harin bai rutsa da kowa ba.

A daya bangaren kuma, kungiyar “the Syrian Observatory for Human Rights” mai sa ido kan yanayin hakkin dan Adam a Syria ta ce, Isra’ila ta kai harin ne yankin Kisweh dake kudancin Damascus, inda mayakan darikar shi’a masu goyon bayan Iran ke da mazauni.

Kungiyar mai mazauni a Birtaniya ta kara da cewa, dakarun Syria sun yi nasarar kakkabo galibin makaman, in ban da biyu da suka fada kan sansanin. (Fa’iza Mustapha)